

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Jihar Dr.Mustapha Muhammad Inuwa,yace ba wai an sanya dokar shawo kan matsalar tsaro bane domin kuntatawa al’ummar Jihar.
Dr.Mustapha Muhammad Inuwa na magana ne a sa’ilinda yake zantawa da manema labarai tare da yi masu bayani akan nasarorinda aka samu sakamakon sanya dokar.
Dokokin dai sun hada da katse layukan sadarwa a wasu Kananan Hukumomi da matsalar tsaro tayi kamari da hana sayar da man fetur a jarkoki a fadin Jihar sai hana dauko icce saga dazuka gami da hana chajin wayar hannu a wasu Kananan Hukumomi tare da takaita zirga-zirga a fadi Jihar.
Dokar wadda ta shafe kusan watanni 3 da sanyawa a halinda make ciki ta haifar da da mai ido ta fuskar takaita aikace-aikacen yan bindiga dadi da masu garkuwa da mutane a jihar,kamar yadda Dr.Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana.
Ya kara da cewar,a sakamakon sanya wannan doka ta bai daya da Jahohinda ke fuskantar matsalar tsaro suka yi ana matukar samun raguwar hare-haren yan bindiga.
Daga nan sai ya bukaci al’umar jihar akan kada su gajiya wurin cigaba da goyon bayan dokar domin ganin an gudu tare an tsira tare son ganin jihar ta dawo da zaman lafiya da aka santa da shi.
Wakilin Jaridar The Fact 24 ya ruwaito cewar har a lokacin hada wannan rohoto babu wata sanarwa ta tsaida dokar,Wanda hakan me nuni da cewar babu takamaiman ranarda dokar zata daina aiki.
#Fact 24

Allah ka kawo Mana zaman lafiya mai dorewa a kasarmu najeriya da sauran sassan duniya!