
Mutune Miliyan 40 Da Suka Fi Kowa Talauci a Najeriya Za Su Samu Tallafin Naira Dubu Biyar-biyar Daga Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya zata rabawa ƴan Najeriya mutum miliyan 40 tallafin naira dubu biyar-biyar kowannensu a maimakon tallafin man fetur.
Ministar kuɗi Zainab Shamsuna Ahmad ce ta sanar da hakan, inda ta bayyana cewar wanda suka fi fama da talauci ne za a bawa tallafin kuɗin a Najeriya.
“Ba za mu iya cigaba da bayar da tallafin man fetur ɗin ba saboda yana illa ga tattalin arzikin ƙasar, saboda haka ma a tsakiyar shekarar 2022 ne za a cire tallafin man fetur ɗin gaba ɗaya.” Inji Shamsuna
_Idon Mikiya

Hakan yyikyau
Alright