
Tare da rahoton Mobile Media Crew

A ranar litinin 18/04/2022 ne kungiyar Baba Buhari “FOR ALL” ta mika ma Gwamnati Jihar Katsina buhunnan shinkafa dubu goma domin tallafa ma ‘yan gudun Hijra da mabukata da nifin rage masu radadi a wannan lokaci na azumin watan Ramadan.
Shugaban kungiyar na shiyyar Arewa maso yamma Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Malumfashi da Kafur, Hon. Babangida Ibrahim Mahuta Talau,
Wanda ya samu wakilcin Shugaban karamar hukumar Malumfashi , Malam Maharazu Dayi ya mika tallafin ga Alhaji Muntari Lawal Shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati Jihar Katsina a madadin Gwamnatin Jihar.
Da yake gabatar da jawabinsa yayin da yake mika tallafin, Hon. Maharazu Dayi ya bayyana cewa, wannan tallafi ne da kungiyar Baba Buhari “FOR ALL” ta saba badawa duk shekara ga mabukata musamman irin wannan lokaci na azumi.
A nashi jawabin yayin da yake amsar kayan tallafin, Alhaji Muntari Lawal ya yaba tare da gode ma kungiyar, akan wannan tallafi da ta bada, ya kuma yi kira ga hukumar bada agajin gaugawa ta Jihar Katsina, da ta raba wannan tallafi ga wadanda abun ya shafa cikin hanzari, duba da halin kunci da Al’umma suke ciki.
Taron bada tallafin da aka gudanar a tsohon ofishin hukumar bada agajin gaugawa ta Jihar Katsina dake kofar soro, ya samu halartar Mai baiwa Gwamna shawara akan harkokin siyasa Kabir Shu’aibu Charanci da wakilai daga hukumar bada agajin gaugawa.
