

A yau Talata 19-4-2022 ne, sabon aakataren Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adu da Al’amurran cikin gida ta Jahar Katsina Alh. Sani Bala Kabomo Wanda kafin nan shi ne shugaban gidan Radiyon Jahar katsina ya kama aiki a sabon ofisjinsa.
Da yake jawabi a yayin mika ragamar aikin, tsohon sakataren mai barin gado
Alh. Musa Sulaiman Matawalle ya yi godiya ga Ma’aikatansa akan yadda suka bashi hadin kai a yayin aiki, sannan ya yi fatan zasu bada cikakken hadin kai da goyon baya ga Sabon Sakataren.
Shi ma Sabon Sakataren Alh. Sani Bala Kabomo ya yi jawabinsa inda ya yi godiya ga Allah akan wannan sauyi tare da fatan samun hadin kai ga Ma’aikata wannan gida domin kawo cigaban ayyukan wannan ma’aikata da jiha baki daya.
Shi ma a nasa takaitaccen jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar ta yada Labarai Alh. Abdulkareem Yahaya Sirika, ya yi jawabinsa inda ya nuna jin dadin aiki da shi tare da nuna cewa, sun dade tare tun ba a wannan ma’aikata ba da tsohon sakataren, sannan ya yi masa fatan Alkairi. Aanna ya yi maraba da sabon sakatare tare da yin fatan samun nasara ga Sabon Sakataren.
Bikin ya sami halartar manyan daraktocin ma’aikatar da shugabannin bangarorin ma’aikatar da suka hada da gidan radiyon jihar da gidan talabiji KTTV da ma’aikatar wallafa ta jihar watau government printing press, da kuma bangaren yada al’adu na jihar Katsina.
