

Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Alhaji Aminu Bello Masari , ya amince da nadin Alhaji Muntari Lawal a matsayin mukaddashin sakataren gwamnatin jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na kafofin yada labarai na zamani, Al-amin Isa.
Wannan nadi ya zo ne bayan aje mukamin ne da tsohon sakataren gwamnatin Alhaji Mustapha Inuwa ya yi ne domin tsayawa takarar neman kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa.
