

Cikin Hutuna Fitowar Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Dr Abdulmumini Kabir Usman CFR, daga fadarsa a Unguwar Ƙofar Soro, domin halartar bikin hawan barakin ƙaramar Sallah da za a gudanar a tsohon gidan gwamnatin jihar Katsina.
Shekara 4 kenan rabon da a gudanar da bikin hawan Sallah a katsina sakamakon matsalolin rashin tsaro da cutar sarƙewar numfashi ta Covid-19 da aka fuskanta a baya.
