

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga ‘yan siyasa da su dauki turbar da za ta tabbatar da ɗorewar siyasa da kuma zaman Najeriya ƙasa ɗaya mai al’umma ɗaya.
Masari ya yi wannan kiran ne a jawabin da ya gabatar lokacin da ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Ribas, kuma mai neman zama ɗantakarar shuganancin kasa a tutar jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa na shekarar 2023.
Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, fitowar mutane irin su Gwamna Wike neman takarar Shugabancin ƙasa, alama ce dake nuna cewa ƙasar nan a ɗunke take ta yadda har kowa zai iya neman shugabancin ta ba tare da fargabar ɓangaren da ya fito ba.
Gwamna Masari, ya kuma yabawa Gwamna Wike a kan irin matakan da ya ɗauka wajen daƙile yunƙurin masu neman kafa ƙasar Biyafara, na hana su samun gindin zama a jihar ta Ribas, wanda da sun sami wannan dama, to da Allah kadai ya san halin da ake ciki yanzu a wannan yanki.
Haka kuma, ya bayyana cewa, ba zai taɓa mantawa da irin goyon bayan da ‘yan Majalisar Tarayya masu wakiltar jihar Ribas suka bashi ba a lokacin da yake shugaban majalisar Wakilai ta Tarayya.
Sai gwamna Masari ya yi ma Gwamna Wike tare da tawagar tashi fatar alkhairi.
Wanda ke jagorantar rundunar yakin neman zaben Gwamna Wike, t<span;>sohon Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hasan Dankwambo, <span;> ya shaida ma Gwamna Masari cewa, sun zo Katsina ne domin ganawa da wakilan jam’iyyar PDP na jihar da za su halarci taron jam’iyyar na kasa domin neman goyon bayan su.
A nashi bangaren, Gwamna Wike ya yi godiya ta musamman ga Gwamna Aminu Bello Masari domin irin tarbar da ya yi masu duk kuwa da cewa basu sanar da shi batun ziyarar kan lokaci ba. Ya kuma sha alwashin ba zai taba mantawa da wannan karamcin ba.
Daga nan tawagar ta Gwamna Wike ta je hedikwatar jam’iyyar PDP ta jihar Katsina domin ganawa da shugabannin jam’iyyar amma cinkoso ya hana sai dai ya tafi bai gansu ba.
