
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta sake samun nasarar ceto wasu mutane goma sha biyu da wasu masu safarar mutane ke yunƙurin tsallakawa da su daga Najeriya zuwa ƙasar Libya ta hanyar amfani da iyakar Najeriya-Niger.
Waɗanda aka ceto ɗin sun fito ne daga jihohin Kwara da Oyo da Edo da Osun da Ondo da kuma Ogun.
Kakakin rundunar SP Gambo Isah ya bayyana haka a yayin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Katsina. Ya kara da cewa, an ceto mutanen ne a ranar Litinin, 2 ga watan Mayu na wannan shekarar da misalin ƙarfe 12:30 na rana a gidan wani mutum mai suna Yahaya Dahiru dake ƙauyen Kalgo na ƙaramar hukumar Daura dake jihar Katsina, sakamakon wasu bayanan sirri da jami’an tsaron ‘yan sandan suka samu.

Wannan nasarar na zuwa ne kwanaki kadan bayan nasarar da rundunar ta samu a jihar na ceto wasu mutune 15 daga hannun wasu masu safarar mutane a garin Daura. Kakakin ya ce, tuni rundunar ta fara gudanar da bincike, domin kamo mai gidan da aka sauke mutanen da kuma Direban motar da ya ɗauko su wato Mas’udu Dusha wanda ke zaune a ƙauyen ‘yan kara dake cikin ƙaramar hukumar Mai’adua.
A karshe kakakin ya ce za a mika mutanen da aka ceto ga Hukumar yaƙi da fataucin Bil’adama ta kasa (NAPTIP) domin gudanar da aikin ta.
