
Gwamnatin jihar Katsina ta amince da bada aikin samar da magudanun ruwa da zai lakume sama da naira Biliyan hudu a garuruwa arba’in da biyu a fadin jihar Katsina.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana hakan a jiya Talata 10/5/2022, a lokacin da yake kaddamar da sabon aikin da ya bada na garin Kabomo dake Karamar Hukumar Bakori. Gwamna Masari ya cigaba da cewa, Gwamnati ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta cigaba da aikin gina magudanun ruwa da yake ceto rayuwar al’umma da dukiyoyin su musamman a yankunan karkara da suka fi samun barazanar zaizayar kasa da roshewar gidaje a lokacin damina, duba da yadda gine- ginen su yake, ya kara da cewa, yin wannan aikin nada matukar mahimmanci duba daminar da ta wuce an ga alfanun wannan aiki da aka yi a kashi na farko da na biyu da na ukku har zuwa na hudu, “domin munga yadda ruwa ya samu hanya ba tare da ya yi ma wadanda aikin ya sha fa barna ba,” ya kara da cewa, ” wannan ne ya bamu kwarin gwiwar cigada da aikin a kashi na biyar domin a cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga barazanar ruwan sama. Ta haka ne wadanda basu amfana da aikin a kashi na farko zuwa na hudu ba, suma yanzu su amfana,” gwamnan ya kara bayyana cewa, wannan aiki yana taimakawa wajen samun ilimi da noma da tsabtar muhalli tare da inganta shi. “A bisa haka ne nake sheda ma al’ummar garin Kabomo cewa, a yau cikin ikon Allah a gaban idonku zamu kaddamar da bada aikin fidda muku hanyar ruwa a karkashin ma’aikatar muhalli ta jiha, ga dan kwangilar da zai yi aikin wanda zai ci kimanin naira miliyan dari da daya, saboda haka akwai bukatar sa ido ga wannan aiki naku, da fatan Allah ya sa ayi aiki lafiya a gama lafiya.” In ji gwamnan.
