
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan jam’iyyar sa ta APC su marawa dan takarar su Bola Tinubu baya don samun nasarar zaben 2023.
Shugaban ya ce marawa Tinubu baya zai taimaka wajen cigaba da manufofin gwamnati na aiyukan raya kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Zaben wanda ya zowa magoya bayan mataimakin shugaban Yemi Osinbajo da bazata, ya sa muhimmancin ziyarar manyan ‘yan jam’iyyar don hada kai.
Tinubu wanda ya nuna mamaki yanda wasu na kusa da shi ko wanda ya yiwa alheri irin shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, amma su ka yi takarar tikitin APC da shi, ya godewa duk wanda ya mara ma sa baya ya na mai nuna kwarin guiwar samun nasara.
Shugaban hukumar zabe Mahmud Yakubu ya ce na’urar tara sunayen ‘yan takara za ta rufe kirib ranar 15 ga watan nan ga ‘yan takarar jihohi sai kuma ta rufe ran 17 ga wata ga ‘yan takarar taraiya.