
Yayin da alhazai da dama su ka sauka a Saudiyya, kasar ta kara rage matakan takatsantsan kan yaduwar cutar korona bairos.
A yanzu dai ba za a tilasta kowa ya sa kyallen rufe hanci ba a wajaje masu rufe ko filaye illa dai a babban masallacin dakin ka’aba da kuma na Manzon Allah da ke Madina.
Hakanan ba za a tambayi takardar rigakafi na yayin shiga jirgi ko motocin sufuri da sauran su.
Tuntuni an samu nasarar daidaita sahu ba kamar yanda a baya a ke barin tazara mai yawa tsakanin masu sallah ba.
Matakan dai sun taimaka wajen barin alhazai daga kasashen duniya su samu gudanar da aikin hajjin bana kuma hakan ya faru ba tare da tsangwama ba.
Please follow and like us: