
Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar katsina a yau ta rarraba ma jami’an Hukumar dake kula da Shiyyoyin ta uniform da kana Nan jikkuna domin rabawa ga Maniyyatan ta Dake fadin jihar Nan.
Insha Allahu zuwa gobe Alhamis da izinin Allah kowane maniyyaci Aikin Hajjin wannan shekarar watau(2022 Hajj) zaya karbi uniform da karamar jikkar shi domin cigaba da shirye shiryen tafiyar su kasa Mai tsarki.
Ana sa ran za’a fara Jigilar Maniyyatan jihar katsina zuwa kasa maitsarki a ranar 22 ga wannan watan idan Allah ya kaimu lafiya da fatan dukkan Maniyyatan mu zasuyi Hajj Mabrur.
Please follow and like us: