
Fasinjojin da ke cikin jirgin na Overland Airways daga Ilorin zuwa Legas a ranar Laraba, an ba da rahoton cewa sun sauka ne bayan da jirgin ya samu wani yanayi mai tsananin zafi a kan daya daga cikin injinsa
Wasu rahotanni sun ce daya daga cikin injinan ya kama wuta ne a lokacin da yake cikin iska, yayin da wasu suka ce lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin ke gab da sauka.
Ma’aikatan jirgin sun dauki matakai don irin waɗannan yanayi marasa kyau kuma sun kwashe fasinjojin nan da nan, Business Day ta ruwaito
A wata sanarwa da Overland ta fitar, ta bayyana cewa a cikin jirgin akwai fasinjoji 33 da suka sauka bayan da jirgin ya tsaya a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.
Kamfanin jirgin ya ce, “Babu wani fasinja da ya ji rauni ta kowace hanya.”“Overland Airways na jinjinawa kwararrun hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN); Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya, (NAMA); Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya, (NCAA) da Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya, (AIB-N) wadanda suka yi gaggawar da kwantar da hankali,” inji shikamfanin jirgin saman