
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya ce Amurka ce ke bayan kudurin kin jinin Tehran na baya-bayan nan, wanda hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta amince da shi, domin matsawa Iran lamba a tattaunawar Vienna.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Iraki Fuad Hussein a ranar Alhamis, inda bangarorin biyu suka kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma ci gaban yankin.
Tun a watan Afrilun shekarar da ta gabata ne aka fara tattaunawa a babban birnin kasar Ostiriya da nufin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, wadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da ita a watan Mayun 2018, tare da laftawa Iran jerin takunkuman karya tattalin arziki.
Tattaunawar da ke dai ta shiga rashin tabbas, bayan da Amurka ta ce ba za ta cire dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran ba a cikin jerin kungiyoyin da take kallo a matsayin na ‘yan ta’adda, wanda yana daga ciikin jerin da Iran ta gabatar na cimma yarjejeniya kafin ta dakatar da matakan data dauka na jingine aiki da wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma da ita a 2015, musamman batun tace sinadarin uranium.
© Hausa Tv Tehran