
Sabuwar Jam ’iyyar adawa ta NNPP tace ba zata zauna ta zuba idanu gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, na kassara jihar Kano ba, musamman a kokarinsa na karbo bashin kudi Naira Biliyan 10 daga bankin Access, domin saka na’urorin sirri a jihar,
Suna ganin kamata yayi Ganduje ya yi abin da yake dole kafin ya tunkari irin wannan aikin, a cewar jam’iyyar.
Wannan Jawabin na kunshe cikin wata sanarwa da Suka aika wa manema labarai, ciki harda Nasara Radio, mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar ta NNPP na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, inda sanarwar tace, Ganduje yana amfani da kujerarsa wajen kassara goben al’ummar Kano da ‘ya’yansu, domin hatta kudin makaranta ya gagara biya, dalilin haka yara da dama sun hakura da karatu a fadin jihar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ba daidai ba ne Ganduje ya watsar da abin da ya shafi damun al’umma ba, kamar karancin ruwan sha da sauransu, ya tafi aikin da tuntuni tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya samar da makamantansu wadannan Kyamarori a lokacin mulkinsa, kuma kowa ya san cewar gwamnatin Ganduje ba zata iya rike ragamar kula da wadannan Kyamarori ba.
“Jam’iyyar NNPP na bada shawara ga ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, su daina bawa Ganduje damar karbo irin wadannan bashi, ya kamata yan majalisa su dinga duba bukatun al’umma kafin aiwatar da irin wannan, domin muna sane da yadda a baya ya karbo bashin Biliyan 15 na harkar ilimi, amma aka karkatar da kudin, an kai matakin da jarabawar daliban aji 6 na firamare (Common Entrance) ta gagara a Kano.
“Mu muna zargin ma zai karbo bashin ne domin maye gurbin abinda aka rasa a yayin zabukan fidda gwani da suka gabata, saboda haka shi kansa bankin Access da sauran bakuna muna kiransu da su kiyayi bawa Ganduje bashi.”
© Nasara Radio