
Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace yana da kyakykyawan fatan samun nasara a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa, don haka bazai janyewa dan takarar PDP Atiku Abubakar ko kuma APC Bola Ahmed Tinubu da sauransu ba, musamman ma yakinin da yake dashi akan gyaran dokar zaɓe, wacce yace abu mai wahala ayi masa murdiya, domin dai talakawa suna matukar fata a gare shi.
Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da jaridar Punch, inda yace matukar zaɓe za’ai na tsakani da Allah, to zaiyi wahala su fadi zaɓe, domin akwai muradin talakawa a tare dashi, bisa burinsu na inganta harkokin ilimi, tsaro, hada kan al’umma, da sauran ayyuka na inganta rayuwa a karkashin jam’iyyarsu ta NNPP mai alamar kayan marmari.
“Ba ni da jam’iyyata ne zamu kayar da wadancan yan takara ba, jam’iyya alama ce, talakawa ne zasu fita suyi zaɓe, kuma sun san bambamcin da yake tsakaninmu dasu, domin basu da abinda zasu fadawa mutane don a zaɓe su, sabanin ni da nayi ayyuka na al’umma a baya, an ga irin rawar dana taka.”
#Nasara Radio