
” Ina cike da farin ciki maras misaltuwa da Allah ya sake nuna mana lokacin sake kusantar masallacin Annabin rahama don sauƙe farali bayan shafe shekaru biye ba tare da ziyara ba sakamakon cutar Corona.
Ina kira ga mahajjatan mu da su zama jakadu na gari, kada kuma mu shagalta, mu yi amfani da damar wajen godewa Allah godiya da kuma yiwa jihar Bauchi da Najeriya addu’oin zaman lafiya da yalwatuwar tattalin arziki”
-Gwamna Bala Muhammad
Kai tsaye da yammacin yau alhamis, Gwamna Bala bayan sauƙa a filin tashi da sauƙar jirage na tunawa da Firaminista Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, ya shiga jirgi don bankwana da maniyyatan jihar Bauchi inda ya gana tare da jan hankulan su kan alfanun yiwa ƙasa da jihar Bauchi addu’oi musamman kan tsaro da tattalin arziki.
Ko kun san:
-Gwamna Bala ne ya gina sansanin alhazan jihar Bauchi.
- Asibitin kula da lafiyar alhazai a cikin sansanin.
- Ɗakuna da masauƙin alhazai masu nagarta.
- Kasuwar zamani da ake sayar da kayayyaki da tsarabar Makka.
-Ɗakin taro na musamman don lakca da koyawa alhazai sauƙe farali.
- Tsari na musamman wajen biyan kuɗaɗe don sauƙaƙa wahalhalu?
- Tsari na musamman da ya rage cunkoso da cakuɗa tsakanin mata da maza.
Kafin zuwan Gwamna Bala alhazan jihar Bauchi sun yi fama da wahalhalu daban-daban a gida Najeriya da ƙasa me tsarki, a halin yanzu waɗannan matsaloli sai tarihi.
Allah ya amsa ibadu.
Daga Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani
Yuni 16, 2022.