
Ɗaruruwan Mabiya Ɗarikar Ƙadiriyya daga sassa daban-daban na Jihar Katsina sun gudanar da Mauludin Sheikh Abdulkadir Jilani.
Taron Mauludin wanda Shugaban Ɗarikar Ƙadiriyya na Jihar Katsina, Sheikh Ahmad Tijjani Bayan Day ya shirya, ya samu halartar Manyan Malamai da dama na Jihar Katsina.
An gudanar da Mauludin ne domin karantar da Musulmai akan kyawawan halayen Manzon Tsira Annabi Muh’d S.A.W, tare da karantar da su akan buƙatar da ke akwai na su yi koyi da halayen a cikin lamurran su na rayuwa.
Horizon News Hausa ta ruwaito cewa, taron ya kuma kasance a matsayin wata kafa da ake karantar da mahalartan akan yadda Sheikh Abdulkadiri ya gudanar da rayuwar shi, da irin gudummuwar da ya bayar wurin cigaban Addinin Musulunci.
A lokacin Taron Mauludin na wannan shekara, Malamai da dama sun yi wa’azi akan Asalin Ɗarikar Ƙadiriyya da kuma yadda Manyan Waliyai suka yi bakin kokarin su wurin gina Darikar.
Malaman sun ja hankali ga mahalarta Mauludin akan su ƙara ƙaimi wurin koyi da kyawawan Halayen Annabi Muhammad Tsira Da Amincin Allah su Kara Tabbata a gareshi a dukkan lamurran su na rayuwa domin samun rabauta a nan gidan duniya da gobe kiyama.
Sun kuma yi kira ga mahalartan akan su ƙara ƙaimi wurin rikon aƙida da koyi da ayyukan alkairi na manyan Shehunnai da Malamai da suka gabata domin kawo cigaban Addinin Islama.
Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Ɗarikar Ƙadiriyya na Jihar Katsina, Sheikh Ahmad Tijjani Bayan Day, ya buƙaci mabiya Ɗarikar akan su kara jajircewa wurin Neman Ilimi tare da yin koyi da halayen Annabi Muhammad S.A.W.
Ya ce babu wani abinda zai sa su kasance masu aiwatar da ayyukan bautar Ubangiji yadda ya kamata sai da Ilimi.
Kakaki News