
Dalilin yin kiran yajin aikin shi ne nuna bacin rai game da matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar.
A sanarwar da manyan kungiyoyin kwadago na kasar guda uku suka fitar, sun kuma bukaci karin albashi ga ma’aiakata da kuma wadanda je ritaya, saboda tsadar rayuwa, mai nasaba da hauhawan farashin man fetur da kuma ababen bukatuwa na yau da kulun.
Sai dai Sakatare janar na kungiyar kwadago ta ODT, yayin wani taron manema labarai ya bayyana yajin aikin da gargadi ga gwamnati akan ta dauki matakai akan hauhawan farashin na kayan abinci da kuma man fetur.
Daga
Iran Hausa TV Redio
Please follow and like us: