
A dadin da ake tunanin mutune 16 ciki har da mambobin jami’an tsaron sa-kai na CJTF ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren da ake kyautata zaton mambobin mayakan ISWAP ne suka kaddamar a jihar Borno.
Har-ila-yau, an tattaro cewa, mayakan na ISWAP sun harbe masu sana’ar jari-bola 13 a kauyen Goni Kurmi da ke karamar hukumar Bama a jihar ranar Asabar.
Majiyoyin Jami’an tsaro sun shaida cewa, wadanda suka gamu da tsautsayin sun hada da maza 11 da mata 2.
Ya fada cewa, “mayakan sun zo cikin motoci hudu da kuma wasu a kan Babura inda suka mamaye yankunan tare da kaddamar da hare-haren su na ta’addanci”.
Majiyoyi sun bayyana kuma cewa, “gomannin mutunen yankin sun arce domin tsira da rayukansu”.
Bayan haka, wasu mayaka dauke da muggan makamai da ake zargin ISWAP ne sun farmaki mambobin tsaron sa-kai na CJTF inda suka kashe uku daga cikinsu tare da yin garkuwa da ma’aikatan samar da agaji a karamar hukumar Monguno da ke Kudancin jihar Borno daren ranar Juma’a.