
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) ta bayyana cewa wasu mambobinta sun yanke shawarar rufe ayyukansu ne saboda ba sa son yin asara kamar yadda kuma ba sa son yin aiki a cikin yanayi maras dadi.
Rufe wasu gidajen mai ya haifar da karancin kayayyaki da kuma dawowar dogayen layukan ababen hawa a gidajen man tun dag ranar jiya Litinin.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar IPMAN, Lagos Satellite Depot, Ejigbo, Mista Akin Akinrinade, ga manema labarai a Legas.
Akinrinade ya ce gwamnati ta kayyade Naira 165 a matsayin farashin lita na Premium Motor Spirit (PMS), yanayin da kuma yanayin da ake ciki a kasuwa ya nuna cewa ya kamata a sayar da mafi karancin farashin kowace lita a kan N180 a gidajen mai.
Shugaban na IPMAN ya ce, “Yanzu kamfanoni mai masu zaman kansu sun kara farashi depot na PMS daga N148.17 zuwa N162 kowace lita abin da suke siyar mana kenan.
“Idan ka yi la’akari da kudin da ake kashewa, sufuri da kuma farashin tashoshinmu, za ka ga ko a Legas, mafi karancin man fetur din da za mu iya siyar da mai zai kai kusan Naira 180 kowace lita.’