
Hadakar Kungiyoyin fararen hula da kuma lawyoyi a tarayyar Najeriya sun yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya INEC da ta yi watsi da dukkan yan takaran neman kojerun gwamnati amma basu shiga zaben farko na fidda dan takata ba wato Primaries.
Jaridar leadership ya Najeriya ta bayyana cewa ta sami zantawa da wasu kungiyoyin fararen hula a kasar wadanda suka hada da
Transition Monitoring Group (TMG) da Transparency International(TI) da kuma Civil Society Legislative Advocacy Center (CISLAC).
Kungiyoyin sun bayyana cewa akwai wasu manya-manyan yan siyasa wadanda aka nadasu ba tare da sun shiga zaben farko na fidda guni ba.
Shugaban kungiyoyin fararen hulan Awwal Rafsanjani ya fadawa Leadership kan cewa wadanda suke kaucewa zaben farko sune suke amfana da zaben wanda suke fada da shi.