
Ziyarar Duba
Daga Comr Nura Siniya
Attajirin Ɗan kasuwar nan shugaban kamfanin jiragen sama na Max Air da kamfanin gine gine da tsare tsare na Afdin Construction ya kai ziyarar duba aikin gina katafaren kamfanin siminti da kuma tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatts hamsin 50 da yake ginawa a Moba ta jihar Kogi.
Kamfanin simintin zai riƙa samar da tan miliyan 3 na siminta a kowace shekara tare da taimakawa Najeriya wajen zama ƙasa mai girma tattalin arziƙi domin yin gogayya da ƙasashen da suka cigaba ta fuskar hada hadar kasuwanci a duniya
Duk a cikin ziyarar duba aikin Alhaji Ɗahiru Mangal, ya yabawa ma’aikatan da suke gudanar da aikin da kamfanin da aka baiwa ƙwantiragin akan yanda aikin yake tafiya cikin sauri wanda ake sa ran kammala aikin a farkon shekarar 2024
Kamfanin zai samar da wuraren ayyukan yi ga sama da mutun dubu goma.