
Daga Hadi Bawa
Hakim at Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta a Nijeriya (ICPC), ta gano wasu miliyoyin Nairori da tsohon Hafasan Hafsoshin Sojan Kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya boye a gidansa da ke Abuja.
A Wata majiya mai tushe ta tsegunta wa jaridar SaharaReporters cewa, wani jami’in soja da suka raba gari da Buratai ne, ya sanar da Hukumar ICPC inda aka boye kudaden da aka gano.
Kudaden da yawansu ya kai Naira miliyan dubu da miliyan 85, ana zargin suna cikin wadanda aka ware ne don a siyo makaman da za a yaki Boko Haram da su aka karkatar da su.
Buratai, ya yi ritaya daga aikin soja ne a matsayin Laftanar Janar, kuma ya rike Hafasan hafsoshin sojan kasa na Nijeriya daga 2015-2021.
Majiyoyin ICPC sun tabbatar da cewa jami’an Hukumar sun je gidan Buratai da ke Yankin Wuse ne da ke daura Jami’ar NOUN da ke Abuja ne a makon jiya bayan wani na hannun daman tsohon Janar din ya tsegunta masu.
SaharaReporters ta fahimci cewa wadannan kudade masu nauyin da aka gano wani bangare ne na biliyoyin Naira da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ware domin siyen makaman yaki da ‘yan ta’adda.
“A ranar Talatar makon jiya ne jami’an Hukumar ICPC suka yi dirar mikiya a wani gida da ke yankin Wuse da ke daura da Jami’ar NOUN, inda suka kama wani da ake kira Kabiru Salisu, yayin da, suka gano miliyan 850 a cikin gidan.
“Ya yi ikirarin gidan na Tukur Yusuf Buratai ne da ke Kwatano a wannan lokacin.
“Jami’an Hukumar ICPC sun tisa keyarsa, zuwa wani ofis din kuma, inda suka sake gano Naira miliyan 1,000 na daban da wata mota da harsashi bai hudawa kirar BMW, G-Wagon da kudinta ya kai Naira miliyan 450,” in ji majiyar tamu.
A watan Maris, 2021 ne, mai ba shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa an karkatar da biliyoyin Naira da aka ware domin siyen makaman da za a yi amfani da su wajen yakar ‘yan ta’adda a karkashin tsaffin shugannin hafsoshin tsaro da suka gabata.
Wannan fallasar na zuwa ne ‘yan watanni bayan shugaban kasa Buhari ya maye gurbin tsaffin shugabannin hafsoshin tsaron da wasu sabbi.
Baya ga Tukur Yusuf Buratai, sauran shugabannin hafsoshin tsaron da aka canza sun hada da shugaban Ma’aikatar Tsaro, Gabriel Olonishakin; shugaban hafsoshin sojan sama, Abubakar Sadique da shugaban sojan ruwa, Ibok Ibas.
Kamar yadda Monguno ya bayyana, “kudaden da suka bata ko dai an sayi makaman ko ba a siya ba, amma dai sabbin hafsashin tsaron kasa da aka nada ba su ga harsashi daya ba.
“Yanzu shugaban kasa ya kawo sabbin mutane a kan kujerar Hafasan hafsoshin tsaron kasa, ina fatan za su yi abin da ya dace. Duk da yake kai tsaye ba zan iya cewa tsaffin Hufsoshin tsaro sun karkatar da kudaden da aka ware don a sayi makamai ba, amma dai sun bata bat. Ba mu san yadda aka yi ba, kuma zuwa yanzu ba wanda zai iya fadin yadda aka yi,” in ji shi.
“Ina da tabbacin shugaban kasa zai binciki lamarin. Ya zuwa lokacin da nake magana da ku, ita ma kungiyar Gwamnoni tana mamakin inda duk kudaden nan suka shige. Shugaban kasa ba zai dauki maganar nan da wasa ba,” ya tabbatar.
“Hasali ma sakamakon binciken sharar fage da aka yi ya nuna kudaden sun bata, su ma kayayyan aikin da aka tsara za a siyo ba a gan su ba. Sabbin hafsoshin tsaro da suka shiga ofis su ma sun ce ba su ga komai a kasa ba,” in ji Monguno.
Tun a shekarar 2016 jaridar Sahara Reporters ke buga jerin rahotannin da ke fallasa irin manyan kadarorin da Buratai ya mallaka a Dubai ta Hadaddiyar Daular Larabawa da ya siya a tsakanin 2013-2015.
Sai dai a wancan lokacin, tsohon hafsan sojan ya sha musanta wadannan zarge-zargen, tare da tabbatar da cewa kudaden nasa da yake hidimomi da su yana samun su ta hanyar gonar macizai da ya mallaka da ke kan babbar hanyar Abuja-Keffi a Jihar Nasarawa da ke da nisan kilomita 50 daga babban birnin kasar