
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Chris Ngige, ya tabbatar da cewa ba da dadewa ba za a kawo karshen yajin-aikin ‘Yan ASUU. The Cable ta rahoto Ministan yana mai cewa malaman jami’o’in gwamnati da suka yi wata da watanni su na ta faman yajin-aiki, za su koma bakin aiki.
Ministan ya bayyana wannan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajen manema labarai bayan an kammala taron FEC a Aso Villa.
An tambayi Chris Ngige game da yajin-aikin kungiyar, sai ya nuna an kusa bude makarantu. Ministan ya ce gwamnati za ta koma zama a ranar Alhamis. Ngige ya ce gwamnatin Muhammau Buhari za ta duba abubuwan da suka jawo aka rufe jami’o’i, domin warware su. “Ba za a dade ba za a shawo kan lamarin. Za a shawo kan yajin-aikin ba da dadewa ba.”
“A cikin matsalolin da ake fama da su sun shafi harkar kudi, albashin ma’aikata, jin dadi da walwala ne.”
“Mun yi zaman sulhu tare da gayyatar ma’aikatar kudi, ofishin kasafin arzikin tarayya, hukumar albashi na kasa da ma’aikatansu a ranar 1 ga watan Maris.” “Bayan nan sai ya bayyana cewa akwai sauran abubuwa biyu da suka rage – batun tsarin albashinsu kamar yadda aka yi tun a yarjejeniyar shekarar 2009.”
“Yarjejeniyar ta ce duk bayan shekaru biyar, za a sake duba albashinsu, wannan magana ta tsaya.