Yau da kullum-Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce ba zai yi kasa a gwuiwa ba wajen neman Sufeto-

Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba ya fitar da sammacin kama Godwin Emefiele, wanda shi ne gwamnan babban bankin kasar. Wannan gargadin ya biyo bayan kin bayyana gaban majalisar a dalilin gayyatar da ta mika wa gwamnan. Mista Gbajabiamila ya sanar da haka ne a ranar Alhamis bayan da Alhassan Doguwa, shugaban masu rinjaye […]

SHUGABA BUHARI YA NADA SOLOMON ARASE YA ZAMA SHUGABAN HUKUMAR ‘YAN SANDA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura sunan tsohon babban sufeton ‘yan sanda Solomon Arasae gaban majalisar dattawa don tanatncewa ya zama sabon shugaban hukumar kula da ‘yan sanda. Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ya gabatar da takardar shugaban kan nada Arase. Tsohon sufeton dai wanda ya fara aiki zamanin tsohon shugaba Jonathan ya kammala […]