BABBAN BANKIN NAJERIYA BAI AMINCE DA KARA WA’ADIN DAINA AIKI DA TSOFFIN KUDI BA

author
0 minutes, 35 seconds Read

Babban bankin Najeriya CBN bai amince da kara wa’adin dakatar da amfani da tsoffin kudi ba daga ranar 31 ga watan nan.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ba da tabbacin lalle bankin ba zai kara wa’adin ba don haka gara duk mai tsoffin kudin ya hanzarta kai su banki.

A taron manema labaru a bankin Emefiele ya baiyana matsayar bankin ta daina amfani da tsoffin kudin da zarar wa’adin ya cika.

Duk da haka majalisar dattawa da wakilai sun sake bukatar bankin ya tsawaita wa’adin zuwa ranar 31 ga watan yuli.

Tuni har wasu ‘yan kasuwa sun daina karbar tsoffin kudin don gudun kar su kasa shigar da kudin banki gabanin karewar wa’adin.

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *