Kotun sauraron karar zabe a jihar Osun za ta yanke hukuncin karar da tsohon gwamnan jihar Gboyega Oyetola ya shigar don kalubalantar aiyana gwamna mai ci Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zabe.
Kotun ta ba da sanarwar a birnin Oshogbo ta hanyar manna takardar sanarwa a kofar shiga kotun cewa za ta yanke hukuncin a ranar jumma’ar nan da karfe 9 na safe.
Oyetola na APC ya sa kafar wanda daya da sabon gwamna Adeleke na PDP a kotun da nuna sam bai lashe zaben ba.
A na ta samun matakai na nuna ba sani bas abo daga gwamna Adeleke kan tsohon gwamna Oyetola ciki har da umurnin dawo da motocin gwamnati da tsohon gwamnan ya tafi da su.