SHUGABA BUHARI YA NADA SOLOMON ARASE YA ZAMA SHUGABAN HUKUMAR ‘YAN SANDA

author
0 minutes, 36 seconds Read

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura sunan tsohon babban sufeton ‘yan sanda Solomon Arasae gaban majalisar dattawa don tanatncewa ya zama sabon shugaban hukumar kula da ‘yan sanda.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ya gabatar da takardar shugaban kan nada Arase.

Tsohon sufeton dai wanda ya fara aiki zamanin tsohon shugaba Jonathan ya kammala aiki har zuwa ga ritayar da a zamanin shugaba Buhari.

In za a tuna tsohon shugaba Jonathan ya nada Arase bayan ya kwabe tsohon babban sufeto Sulaiman Abba wanda a ke ganin ya taka rawa wajen gudanar da zabe mai adalci a 2015 da hakan ya sa shugaba Buhari ya lashe zabe.

Yanzu dai ya nuna Arase zai maye gurbin Muslihu Smith wanda ya yi murabus daga shugabancin hukumar.

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *