
Daga Suleiman Ahmad
Kwamishinan Ilmi Mai Zurfi na Jihar Gombe, Mr. Meshack Audu Lauco, da na Yada Labarai da Al’adu, Julius Ishaya Lapes, sun jinjina wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, saboda ayyukan ci gaban kasa da ya samar a cikin shekara uku da ya yi a kan karagar mulki.
Hon. Lauco, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe, ya ce, “Gwamna Muhammad Inuwa ya zama abin alfari ga duk wani mutumin Gombe, saboda irin ayyukan raya kasa da ci gaban da ya kawo a Jihar ba tare da wani bambacin siyasa ba.”
Ya lissafo wasu daga cikin ayyukan raya kasa da Gwamna Inuwa ya yi wa jama’ar Jihar Gombe da suka hada da gina manya tituna da sa masu fitilun hanya masu amfani da hasken rana da kuma kammala katafariyar tashar motaci ta zamani, wadda za ta rika daukar motoci 3,000 a lokaci daya da kuma bangaren manyan motoci na tirela kusan 2,000 domin samar da saukin ga matafiya.
Kazalika ya ce, Gwamnan ya gina asibiti da masallatai guda biyu manya da kuma ofishin ‘yan kwana-kwana da na ‘yan sanda duk a cikin wannan katafariyar tasha ta zamani.
Hon. Lauco ya kara da cewa Jihar Gombe karkashin jagoranci Gwamana Muhammad Inuwa Yahaya ta samar da fili kadada 1,000 don gina rukunin masana’antu a Dadin Kowa da ake Karamar Hukumar Yamaltu Deba, wadda babu irin ta a fadin kasar nan.
“Yanzu haka ana kan aikin samar da hanyoyi da sauran kayan ci gaban masana’antu a wannan katafaren wurin da ake kira da “Muhammad Buhari Industrial Pack”, in ji shi.
Shi kuwa Kwamishinan yadda Labarai da Al’adu, Hon. Julius Ishaya Lapes, kira ya yi ga jama’ar Jihar Gombe su kalli irin ci gaban da Gwamna Muhammad Yahaya ya kawo a bangarori daban-daban na rayuwa.
Ya ce kara da cewa, Gwamnan Gombe ya gama gyara babban asibitin Jihar da na Bojude, Nafada, Kaishingi da kuma Dadin Kowa, duk sun samu kyakyawan kulawa.
Haka zalika ya ce duk masoyin ci gaban Gombe zai yaba da irin ayyukan Gwamna a bangaran ilimi da raya kasa da habaka tattalin arziki da kuma ci gaban matasa ta hanyar sama masu sana’o’in ci gaban rayuwa.