
Ahmad Rabe Yanduna
‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da kananan yara guda uku a karamar hukumar Ajaokuta da ke jihar Kogi inda suka nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 100.
Jaridar
DCL Hausa ta bibiyi Channels TV wanda ya ce jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Ayah, ya tabbatar da sace mutanen a ranar Juma’a.
A wata sanarwa da ya fitar, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Edward Ebuka ya tura jami’an ‘yan sanda daban-daban da ke yaki da masu garkuwa da mutane tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarauta domin zakulo masu garkuwa da mutane domin kubutar da yaran.
Yaran uku ne akai garkuwa da su masu shekaru tsakanin uku, biyar, da shekaru goma a yammacin Larabar da ta gabata da misalin karfe takwas na dare a gidansu na Kaduna Estate Ajaokuta Steel Township, da wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance su ba.