Motar mai ɗaukar kimanin matane 30 za ta riƙa gudanar da aikin Jigilar Likitoci daga Asibitin da ke Katsina zuwa Asibitin Karamar Hukumar Mashi.
A lokacin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da motar shugaban Asibitin Dr. Suleiman Bello yace, Gwamnatin Jihar ta bayar da motar ce,domin ɗaukar Likitoci daga nan Katsina zuwa Asibitin Garin Mashi, domin riƙa gudanar da ayyukan su a can.
Dr. Suleiman Bello ya ƙara da cewar, yanzu haka Gwamnati ta samar da dukkanin wasu kayayyakin aiki a Asibitin ta Garin Mashi, domin rage cinkoson majinyata da ke kwance a Asibitin koyaswar ta Katsina.
Haka kuma ya ba da tabbacin cewar, za’a riƙa gudanar da ayyukan kula da marassa lafiya da suka haɗa da, tiyatar ko wane irin ciwo wato, (surgery) da sauran su, domin samawa al’umma sauƙi, musamman waɗanda ke zaune a shiyar Daura.
Kazalika yace, ana san ran nan da shekaru shidda masu zuwa za’a fara yaye ɗalibai a ɓangarori kiwon lafiya daban-daban, sai kuma ya koka gameda Ɗalibai dake ka karantar aikin Likitanci, sai su tafi ƙasashen ketare domin yin aiki a can.
Modern Journalists!
#sdkGwanatin Jihar Katsina ta samar da babbar motar asibiti.

#sdk